Fashola, ministan ayyuka, yayi bayanan kokarin gaggawa kan gadar Wukari da ta fado

Fashola, ministan ayyuka, yayi bayanan kokarin gaggawa kan gadar Wukari da ta fado

- Yace shugaban kungiyar kiyaye hadurra, Boboye Oyeyemi, ya tura jami'ai gurin da abin ya faru don saukake canza hanyar wucewa

- Fashola yace za a sanar da masu abin hawa da sauran mutane duk cigaban da aka samu na aikin gaggawar

- Yace an bada kwangilar yin gyaran gaggawa don a rage cunkoso a titin

Fashola, ministan ayyuka, yayi bayanan kokarin gaggawa kan gadar Wukari da ta fado
Fashola, ministan ayyuka, yayi bayanan kokarin gaggawa kan gadar Wukari da ta fado

Babatunde Fashola, Ministan wuta, aiyuka da gidaje ya sanar da faduwar gadar da ta hada Jalingo da Wukari a maraban Gassol a jihar Taraba.

A bayanin Fashola, wanda daraktan watsa labarai na Ma'aikatar yasa hannu a Abuja, Theodore Ogaziechi, yace, al'amarin ya faru ne bayan ruwan saman da aka yi a ranar laraba da yammaci.

Yace an bada kwangilar yin gyaran gaggawa don a rage cunkoso a titin.

Ministan ya hori masu abin hawa dasu yi amfani da hanyar Jalingo - Garba Cheda - Bali-Takum-Katsina Ala cewa da za a fara gyaran a ranar Alhamis.

Yace shugaban kungiyar kiyaye hadurra, Boboye Oyeyemi, ya tura jami'ai gurin da abin ya faru don saukake canza hanyar wucewa.

Fashola yace za a sanar da masu abin hawa da sauran mutane duk cigaban da aka samu na aikin gaggawar.

DUBA WANNAN: Beraye sun tafka barna a wani banki

Gadar dai tana da matukar muhimmanci wajen jona garuruwan dake yankin arewa maso gabas, wadda ke can gefe inda ba safai arzikin kasa ke kai gare su ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng