Yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a cikin barikin Sojojin Najeriya

Yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a cikin barikin Sojojin Najeriya

Wasu gungun mayakan Boko Haram yan kunar bakin wake sun kai farmakin cikin barikin Sojoji mai suna, ‘33 Artillery Barracks’ dake bayan garin Maiduguri a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni, inji rahoton jaridar The Cables.

Wata majajiya na karkashin kasa daga rundunar Sojin kasa ta tabbatar ma majiyar Legit.ng cewa yan kunar bakin waken sun tayar da bama baman ne da misalin karfe 9:30 na dare a wani dandalin shakatawa dake cikin barikin.

KU KARANTA: 2019: Makarfi ya dauki alwashin kawar da Buhari daga kujerar shugaban kasa

Majiyar yace yan kunar bakin waken sun shigo ne a cikin baburan ‘Adaidaita sahu’,; “Maharan sun yi amfani da damar ana barin mutane suna zuwa dandalin dake cikin barikin sakamakon aiki rusau da gwamnatin jihar Borno ke yin a gidajen karuwai da dandalolin shaye shayen giya.

Yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a cikin barikin Sojojin Najeriya
Barikin Sojojin Najeriya

“Kun san gwamnatin jihar Borno na rusa gidajen karuwai da dandalolin shaye shayen giya, don haka sai jama’a daga wajen gari suke shigowa barikin don holewarsu, a haka ne yan bindigan suka shigo suka tayar da bama bamansu a tsakiyar jama’a.” Inji shi.

Haka zalika shi ma wani jami’in kungiyar Sojojin sa kai ta Sibiliyan JTF, Moruma Zannah ya tabbatar da faruwra harin, inda yace jama’a da dama sun mutu, yayin da aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru dake Maiduguri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng