Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban darikar Tijjaniya na duniya, hotuna
A yau, Laraba, ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawagar jiga-jigan jagororin darikar Tijjaniya a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
A jawabin sa ga tawagar Tijjanawan karkashin shugaban tan a duniya, Sheikh Ahmed Tijjani Ibrahim Inyass, shugaba Buhari ya shaida masu cewar burin sa shine kawo cigaba ga kowanne yanki na Najeriya ba tare da la’akari da addini, kabila ko yanki ba.
Kazalika ya mika godiyar sa tare da nuna jin dadi bisa yadda Shehunnan darikar ke yi masa tare da Najeriya addu’o’i.
A jawabin sa, Sheikh Inyass, ya shaidawa shugaba Buhari cewar sun zo Najeriya ne daga kasar Senegal domin yin ta’aziyya ga iyalan shugaban Tijjaniya na Najeriya, Khalifa Sheikh Isyaka Rabi’u, da allah ya yiwa rasuwa kwanakin baya.
DUBA WANNAN: Kasar Amurka ta tiso keyar ‘yan Najeriya 34 gida, akwai dalili
Kazalika ya shaidawa shugaba Buhari cewar, fiye da mutum miliyan 40 magoya bayan darikar Tijjaniya na yiwa shugaba Buhari addu’ar samun nasara a kokarin san a dora Najeriya a kan turbar cigaba mai dorewa.
Kafin su bar fadar shugaban kasar, Sheikh Inyass ya yiwa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya, cigaba da wadatar lafiya ga dukkan ‘yan kasa bakidaya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng