Yadda wani ango ya yiwa amaryar sa kisan gilla wata 4 kacal bayan daura masu aure
Wata ma’abociyar amfani da dandalin sada zumunta na Facebook, Meg Barn, ta tona asirin wani magidanci day a kashe matar sat a hanyar lakada mata dukan tsiya, watanni hudu kacal bayan daura masu aure.
Marigayiyar amarya, Gloria Onyedikachi Obinna, ta gamu da ajalin ta ne sakamakon rikicin cikin gida tsakanin tad a angon ta, Mgbeodinma Samuel, dan asalin garin Awo-Idemili dake jihar Imo.
Da take Karin haske a kan batun kisan, Barn, ta bayyana cewar ango Mgbeodinma ya bar gawar amaryar ta sa Gloria bayan ya kashe ta tare da kin gayawa kowa batun mutuwar ta.
An daura auren Gloria da Mgbeodinma ranar 10 ga watan Fabrairu na shekarar nan, 2018, kuma angon na ta ya yi mata kisan gilla ne ranar Asabar, 16 ga watan Yuni.
Barn bata bayyana abinda ya haddasa rikici tsakanin ma’auratan ba hart a kai ga angon ya hallaka amaryar sa.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa ba zan mayar da ko kwandala ga hukumar EFCC ba – Tsohon gwamnan PDP
Labarin abin da ya samu amarya Gloria ya jawo barkewar maganganu a kan rigingimun cikin gida dake faruwa a tsakanin ma’aurata. A yayin da wasu ke alla-wadai da halin maza da matan dake daukan makami ko dukan aboki ko abokiyar zama idan an samu sabani, wasu kuwa kira suka yi ga hukuma da ta shiga batun yawaitar asarar rayuka da ake samu sakamakon rikici tsakanin ma’aurata.
Barn bata bayyana inda ko halin da ango Samuel ke ciki ba, kazalika ba ta yi Karin bayani a kan ko jami’an tsaro sun shiga cikin maganar ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng