Gwamanan jihar Kaduna a ya bazama nahiyar Turai don neman yan kasuwa su zuba jari a Kaduna

Gwamanan jihar Kaduna a ya bazama nahiyar Turai don neman yan kasuwa su zuba jari a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya shilla kasar Netherland dake nahiyar Turai don neman hadin kan kamfanoni da Attajiran yan kasuwan kasar dasu zuba jari a jihar Kaduna, ta hanyar bude kamfanoni, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hadimar gwamna El-Rufai kan kafafofin sadarwar zamani, Maryam Abubakar ce ta daura hotunan gwamnan yayin da ya kai ziyara zuwa shahararren kamfanin nan dake saka zannuwan Mata, yaduka da shaddodi, wato Vilisco.

KU KARANTA: Yansandan Najeriya sun yi ma wasu gagararrun yan bindiga shigo shigo ba zurfi

Wannan kamfani na Vilisco yana nan ne a yankin garin Helmond, na kasar Netherlands, kuma sun kayayyakin kamfanin nasu sun shahara a tsakanin yan Najeriya, inda suk shagon siyar da shadda ko zani da jake sai ka ga kayan Vilisco.

Da wannan ne gwamnan jihar Kaduna ya nemesu dasu bude masaka a jihar Kaduna, don su dinga saka kayayyakin nasu ba tare da wahala ba, ta yadda zasu matso kusa da masu siyan kayan nasu, kuma kayan zasu yi arha, sa’annan matasa da dama zasu samu aikin yi.

Idan za’a tuna, kimanin shekaru biyu da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani katafaren kamfanin sarrafa abincin kaji a jihar Kaduna, Olams, wanda gwamna El-Rufai ya gayyato su.

Haka zalika gwamnan ya samu nasarar karkato da akalar kamfanin sarrafa dankalin turawa, Vicampro, zuwa jihar Kaduna, inda a yanzu haka sun bude kamfani a yankin kudancin jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel