Mulkin Buhari: Guraben ayyuka 10,291 aka rasa a cikin shekara daya - Rahoto

Mulkin Buhari: Guraben ayyuka 10,291 aka rasa a cikin shekara daya - Rahoto

Akalla guraben ayyuka dubu 5 ne da dari 212 'yan Najeriya suka rasa a cikin watanni shida na karshen shekarar 2017 da ta gabata wanda shine yakawo jimillar yawan ayyukan da aka rasa ya zuwa dubu 10 da dari 291 a shekarar.

Wannan alkaluman dai kamar yadda muka samu, kungiyar masu kamfanonin sarrafa kayayyaki ta Najeriya ce mai suna Manufacturers Association of Nigeria, MAN ta sanar da hakan a cikin wani rahoto da ta fitar.

Mulkin Buhari: Guraben ayyuka 10,291 aka rasa a cikin shekara daya - Rahoto
Mulkin Buhari: Guraben ayyuka 10,291 aka rasa a cikin shekara daya - Rahoto

KU KARANTA: Dattijan Najeriya 4 da suka shawarci Buhari kar ya tsaya takara a 2019

Legit.ng ta samu cewa sai dai kuma rahoton ya nuna cewa akalla guraben ayyukan yi sama miliyan day da dubu dari shida ne suka samu a kasar a cikin lokacin na shekara daya.

A wani labarin kuma, Gidauniyar fitaccen attajirin nan dan asalin arewacin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote watau Dangote Foundation ta kaddamar da wasu rukunin gidaje dari biyu da ta ginawa 'yan gudun hijira dake a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Kamar dai yadda muka samu, rukunin gidajen da suka kunshi gidaje akalla 200 an kuma ce suna kunshe ne da makaranta, asibiti da ma dukkan sauran abubuwan more rayuwa da 'yan gudun hijirar za su bukata.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng