Mahaifiyar Shekau ta tsere daga harin Boko Haram a kauyensu

Mahaifiyar Shekau ta tsere daga harin Boko Haram a kauyensu

- Wannan ne ya nuna cewa Ms Abubakar bata tsallake tashin tashina na ta'addancin Dan ta ba

- A tattaunawar an tambaya matar ko tasan shugaban kasar Najeriya, sai tace a'a

- Da aka tambaye ta ko tasan Muhammadu Buhari, sai tace eh, ta taba Jin sunan

Mahaifiyar Shekau ta tsere daga harin Boko Haram a kauyensu
Mahaifiyar Shekau ta tsere daga harin Boko Haram a kauyensu

Falmata Abubakar, mahaifiyar Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ta dandani harin danta.

A wata hira da majiyar mu ta samo tsakanin Chika Oduah ta muryar Amurka da Ms Abubakar, Ms Abubakar tace bata da masaniya ko Dan ta na raye ko a mace.

Kamar yanda Ms Oduah tace, an tilasta Ms Abubakar komawa kauyen Shekau baya da tayi gudun hijira zuwa wani birnin.

Ta'addancin da Dan ta yake jagoranta itama ya shafe ta. Tana rayuwar ta a wani birni kusa dasu, mai suna Babangida inda Boko Haram suka kawo hari, bata da wani zabi da ya wuce ta koma kauyen Shekau. Inji Oduah.

DUBA WANNAN: Budaddiyar Wasika zuwa ga Hamza Al-Mustapha kan 2019

Wannan ne ya nuna cewa Ms Abubakar bata tsallake tashin tashina na ta'addancin Dan ta ba.

A tattaunawar an tambaya matar ko tasan shugaban kasar Najeriya, sai tace a'a.

Da aka tambaye ta ko tasan Muhammadu Buhari, sai tace eh, ta taba Jin sunan.

Wannan ya nuna irin kasurgumin kauyen da matar take rayuwa.

Ms Shekau tace da yawa mazauna kauyen tsoron ta sukeyi kuma suna gudun mu'amala da ita.

Ta kwatanta kauyen da kauyen kayau wanda yake kilomita da yawa tsakanin shi da babban titi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel