Wani Azzalumi daga 'yan Taliban yayi 'shahada' a hannun bama-baman Amurka a jiya

Wani Azzalumi daga 'yan Taliban yayi 'shahada' a hannun bama-baman Amurka a jiya

- Shine ya kai hari kan Malala Yusufzai lokacin tana shekaru 13

- Sun harbe ta a ka amma bata mutu ba, sai dai tace ta yae musu

- Yana shirin fita sallar idi bam din ya kashe shi da matarsa 'yar shekaru 10

Wani Azzalumi daga 'yan Taliban yayi 'shahada' a hannun bama-baman Amurka a jiya
Wani Azzalumi daga 'yan Taliban yayi 'shahada' a hannun bama-baman Amurka a jiya

A wani harin da Amurka ta kai kan gidan shugaban 'yan Taliban bangaren PAkistan, bayan da ta shafe shekaru gommai tana nemansa ruwa a jallo, tayi nasarar kashe shi yana shirin fita sallar idi bayan gama azumin watan Ramadana a jiya da safe.

Kafar yada labaran kasar Pakistan ta tabbatar da harin, inda kuma tashe, harin, ya kashe iyalinsa mai shekaru 10 da haihuwa, da ma wadansu da basu ji ba basu gani ba, saboda suna makwabtaka dashi.

Shi dai Mullah Fadhlullah, yayi kaurin suna wajen kisan mummuke, kan shugabannin siyasar kasar Pakistan, da ma hare-hare kan yara musamman a makarantun Boko da masu hira a talabijin, kamar dai yadda yayi wa Malala Yusufzai.

DUBA WANNAN: Budaddiyar Wasika zuwa ga HAmza Al-Mustapha

Ya fara shugabantar kungiyar shekaru biyar da suka wuce, bayan da wani hari makamancin wannan ya hallaka tsohon shugaban Taliban din.

Su dai Taliban, kamar Boko Haram, sun shafe shekaru kusan arbain suna fada da gwamnati kan kokarin kawar da mulkin Boko da kawo shari'ar Islama ga jama'ar kasashen Pakistan da ma Aghanistan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel