Gwamnati ta kafa dokar hana shigo da nama garin Abuja, duba dalilin

Gwamnati ta kafa dokar hana shigo da nama garin Abuja, duba dalilin

Hukumar gudanarwa na babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ta saka dokar haramta shigo da danyen nama daga jihohin da ke makwabtaka da Abuja zuwa cikin babban birnin tarayyar.

Sakataren FCTA da ARDS, Stanley Ifeanyichukwu Nzekwe ne ya bayar da sanarwan a ranar Laraba a taron kaddamar da manyan motoccin dakkon nama 22 da a kayi a mahautar Karu da Dei-Dei.

KU KARANTA: A karo na farko, mahaifiyar Shekau tayi magana a kan Boko Haram

Nzekwe ya ce dokar za ta fara aiki nan take inda ya kara a cewa wasu mahautan sukan yanka dabobi ba tare da likitocin dabobi sun duba lafiyarsu ba kuma su shigo da su kwasuwannin Abuja.

Ya ce wannan babban laifi ne kuma galibi irin wadannan dabobin basu da lafiya kuma cin namansu na iya janyo wa mutane cuttutuka da dama. Ya kuma ce duk wanda aka kama yana karya wannan doka zai dandana kudarsa.

Sakataren ya kuma sanar da cewa laifin ne daukan nama a cikin abin hawa wanda ba'a kera shi da karfen da baya tsatsa wato 'stainless steel' a birnin Abuja. Duk wanda aka kama yana jigilar nama alhalin abin daukan namansa ba wanda doka ta amince da ita bane zai fuskanci hukunci.

A jawabinta, shugaban sashin likitocin dabobi na FCTA, Mrs Reguna Adulugba ta ce an samar da sabbin motoccin jigilar naman ne saboda a kiyaye lafiyar al'ummar garin kamar yadda ya ke a sauran kasashen duniya.

Ta kuma kara da cewa gwamnati za ta fara aikin hakkar rafi zuwa gidan gona na kifi kana a samar da ababen zamani da zai taimaka wajen fara kiwon kifin.

"A yunkurin mu na inganta kiwon kifi a Abuja, ma'aikata ta za ta hada gwiwa da wasu masu saka jari wajen gina wajen shakatawa a Maitama inda kuma za'a rika kiwon kifi a wajen," inji ta.

Daga karshe, ta ce an bayar da kwangilar ginin katafaren wajen kiwon kifi kanana kuma an kammala ginin wani wajen kiwon kifin a Gwagwalada.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164