Ba zan iya tabbatar da nagartar hadiman Buhari ba - Keyamo
- Direktan sadarwa na kungiyar yakin neman zaben Buhari, Festus Keyamo ya bayyana cewa Buhari ne kadai ya amince da cewa nagartace ne
- Ya kuma ce zargin da wasu keyi na cewa Buhari 'yan arewa kawai yake bawa manyan mukammai a gwamnatinsa ba gaskiya bane
Direktan sadarwa na kungiyar yakin neman zaben Buhari a zaben 2019, Festus Keyamo (SAN) ya bayyana cewa shugaba Buhari ne kadai ya tabbatar da nagartarsa amma banda sauran hadimansa.
Hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan ne a wata hira da akayi da shi a wata mujalla da ake wallafawa duk wata a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA: Wani mutum mai dauke da cutar kanjamau ya yadda ta ga mata fiye da 200 da gangan
A yayin da yake magana a kan zargin da ake yiwa shugaban na nuna banbanci da kuma daukan aiki da akayi a boye a babban bankin kasa CBN da wasu manyan hukumomin a karkashin gwamnatin Buhari, Keyamo ya ce:
"Ka tuna akwai wani lokaci da ake korafi cewa ana daukan mutane daga wata yanki ne kawai aiki, sai dai bayan wadannan abubuwan sun kai ga kunnen shugaban kasa, wane mataki ya dauka?
"Kana son shugaban kasa ya zauna ya tattara sunayen mutanen da za'a dauka a hukumomi da ma'aikatu ne? Ba za mu iya tabbatar da nagarta mutanen da ke kusa da shugaban kasa ba. Ina fadin wannan a fili kowa ya sani, ba zan iya tabbatar da nagartan masu yi masa hidima ba.
"Lokacin da batun nuna banbanci wajen daukan aikin ya kai ga kunnensa, ya bayar da umurnin a dakatar da daukan aikin."
Kazalika, ya kuma ce ba gaskiya bane zargin da wasu keyi na cewa Buhari yana fifita yan arewa wajen nadin manyan mukamai a Najeriya, ya bayar da misalin shugabanin soji na kasa inda ya ce biyu daga arewa suke sai koma sauran biyu daga kudu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng