Wani mutum mai dauke da cutar kanjamau ya yadda ta ga mata fiye da 200 da gangan

Wani mutum mai dauke da cutar kanjamau ya yadda ta ga mata fiye da 200 da gangan

Jami'an tsaro sun cafkwa wani mutum, Claudio Pinti, da ake kyautata zaton ya yadawa kwayar cutar HIV da ke janyo cutar kanjamau ga fiye da mutane 200 da ya yi jima'i da su a kasar Italy.

Kakakin hukumar yan sandan na birnin Ancona da ke gabashin gundumar Adriatic ya shaidawa dpa a ranar Alhamis cewa an damke Claudio Pinti mai shekaru 35 kwanaki biyu da suka wuce.

Duk da cewa ya san yana dauke da kwayar cutar na tsawon shekaru 11, bai taba sanar da mutanen da ya ke soyaya da su ba inji wata sanarwan da yan sandan suka fitar kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya na daf da kara karbar $500m daga kudaden da Abacha ya wawura

Bayan yan sandan sun damke shi, Mista Pinti ya shaidawa hukumar cewa shi bai ma yarda cewa akwai kwayar cutar HIV da ke janyo AIDS ba a duniya.

Rashin tausayi: An damke wani mutum da ya yadawa sama da mutane 200 ciwon kanjamau da gangan
Rashin tausayi: An damke wani mutum da ya yadawa sama da mutane 200 ciwon kanjamau da gangan

A taron manema labarai da yan sandan suka kira a ranar Laraba, yan sandan sun ce Mista Pinti ma'abocin amfani da shafukan soyaya ne a yanar gizo kuma ana kyautata zaton ya shafawa fiye da mutane 200 kwayar cutar ta HIV.

An dai kama shi ne bayan daya daga cikin wanda su kayi soyaya ta tafi asibiti inda akayi mata gwaji saboda rashin lafiya da ta kamu dashi kuma aka gano tana dauke da kwayar cutar HIV.

Hukumar yan sandan ta gargadi mutane game da shi har ma ta fitar da hotunan Mr Pinti saboda mutane su rika gane shi kafin ya yaudare su nan gaba.

Kakakin hukumar yan sandan ya ce mutane da dama sun kira waya don shigar da kara a kan Mr Pinti kuma ana tantance su. "Mutane suna jan kafa wajen fitowa ne saboda kunya," inji shi.

A wata labari mai kama da wannan da ya faru a shekarar 2017 a kasar Rome, Kotu ya aike da wani mutum mai shekaru 24 zuwa gidan kurkuku saboda yadawa mutane 30 cutar HIV ciki har da wata mai juna biyu wanda itama ta shafawa jaririyar cikin ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel