Inan nan da raina, ku daina cewa na zunduma tekun Legas – Wata mata mai babbar mota
Wata mata da ake zargin ta zunduma cikin tekun Legas bayan ganin motar ta a ajiye a saman gadar Third mainland a jihar Legas ta karyata rahotannin dake yawo a gari.
A kwanakin baya ne kafafen yada labarai da suka hada da Legit.ng suka kawo maku labarin cewar wata mata ta bar motar ta mai tsada a saman gadar sannan ta zunduma cikin teku har jami’an bayar da agajin gaggawa a jihar Legas (LASEMA) suka zo wurin domin tsamo gawar ta daga cikin tekun.
Saidai a jiya, Talata, hukumar LASEMA tayi watsi da rahotannin tare da faifan bidiyon da ake yadawa a kan batub zundumawar matar cikin tekun tare da bayyana cewar, mijin matar ya fita daga cikin motar ne domin kawai bayar da agaji.
DUBA WANNAN: Alade mai nasibi ya hangowa Najeriya nasara a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa (Hotuna)
A wata hira ta wayar tarho da tayi da jaridar Daily Trus, matar t ace da ita da mijinta na nan da ran su cikin koshin lafiya da farinciki tare da bayyana cewar tuni mijin nata ya sanar da hukumomin da suka dace abinda ya faru.
Shugaban hukumar LASEMA, Adesina Tiamiyu, ya bukaci jama’a da suyi watsi da duk wani rahoto ko faifan bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta a kan batun cewar wata mata ta zunduma cikin tekun, domin nba gaskiya bane.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng