Na shiga cikin sana’ar sace mutane ne domin samun kudin hidimar sallah – Wani matashi

Na shiga cikin sana’ar sace mutane ne domin samun kudin hidimar sallah – Wani matashi

Hukumar ‘yan sanda a jihar Naija tayi nasarar cafke wasu matasa guda biyu da suka addabi mazauna yankin Sabon Mariga dake karamar hukumar Kafi da satar mutane domin neman kudin fansa.

Jami’an ‘yan sanda dake aiki a ofishin hukumar na Kagara ne suka yi nasarar cafke matasan biyu; Mohammed Kwairi, mai shekaru 23 da Emmanuel Idili, mai shekaru 21.

An kama matasan ne bayan wasu jama’a sun sanar da hukumar ‘yan sanda cewar, matasan na yiwa mazauna yankin barazanar su biya miliyan N2.5 a cikin wani asusu ko kuma su sace mutum.

Na shiga cikin sana’ar sace mutane ne domin samun kudin hidimar sallah – Wani matashi
Jami'an 'yan sanda

Daya daga cikin matasan, Mohammed, ya shaidawa manema labarai cewar ya shiga sana’ar garkuwa da mutane ne domin samun kudin da zai yi hidimar sallah da su.

DUBA WANNAN: Waka a bakin mai ita: Babu Buhari cikin wadanda suka yi min juyin mulki - Shagari

Ina neman kudin da zan yi hidimar sallah da su ne, ban taba sanin ‘yan sanda zasu kama mu ba. Ran iyayena ya matukar baci har sun yi fushi sun ki zuwa duba nit un bayan kama mu. Gaskiya na yi nadamar abinda na aikata kuma ina rokon iyayena su yafemin,” mohammed ya fada cikin nadama.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Naija, Muhammad Abubakar, y ace nan bad a dadewa ba zasu gurfanar da matasan gaban kotu domin daukan matakin shari’a kan su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng