Gwamnoni 7, Tinubu da Akande sun tsayar da Oshiomhole
Gwamnonin jam’iyya mai mulki wato APC guda bakwai, tare da babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban jam’iyyar na farko, Cif Bisi Akande sun kai ziyarar bangirma ga ofishin yakin neman zaben Adams Oshiomhole, dan takarar shugabancin jam’iyyar dake kan gaba.
Gwamnonin da Oshiomhole ya jagoranta domin zaga ofishin yakin neman zaben sun hada da included Atiku Bagudu, Kebbi; Ibikunle Amosun, Ogun; Rotimi Akeredolu, Ondo; Umar Ganduje, Kano; Tanko Al-Makura, Nasarawa; Simon Lalong, Plateau; da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.
Bagudu wanda yayi hira da yan jaridu yace dukka gwamnonin na farin ciki da dan takarar shugabancin jam’iyyar na kasa wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Edo.
Yace kwarewar Oshiomhole a matsayin tsohon gwamna, shugaban kungiyar kasuwanci, sannan kuma dan rajin damokradiyya sune abubuwan da yasa suka ga zai dace da wannan matsayi domin zai iya taimakawa jam’iyyar APC wajen cimma manufofinta.
KU KARANTA KUMA: Cin hanci da rashawa ne babban hadari ga cigaban Afrika – Shugaba Buhari
Ganduje yace zuwansa na nuna cewa Oshiomhole zai samu kuri’un dukkanin wakilai daga jihar Kano, inda ya bayyana cewa alamu sun nuna shi zaiyi nasara tun kafin zabe.
A nashi bangaren Tinubu yace zuwansa ya nuna cewa yana nan akan bakarsa na daukaka jam’iyyar.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban jam'iyyar APC, John Oyegun ya janye daga takarar sake neman kujerar shugabancin jam'iyyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin samun ingantattun labarai, bide mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng