Ina cikin mutanen da aka zaba domin yin takara da Abiola - Boss Mustapha

Ina cikin mutanen da aka zaba domin yin takara da Abiola - Boss Mustapha

- Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce yana daya daga cikin wadanda aka zaba don takara tare da Abiol

- Mustapha ya bayyana hakan ne a wajen taron karrama wadanda suka sami lambar girma ta kasa da akayi a fadar Aso Villa

- Mustapha ya kuma ce zaben June 12 ce zaben farko da yan Najeriya suka jefa kuri'u ba tare da la'akari da banbance-banbancen kabila, yanki ko yare ba

A jiya Talata ne sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa yana daya daga cikin wadanda aka zaba don yin takarar zaben shugabancin kasa tare da marigayi Cif MKO Abiola wanda ya lashe zaben June 12 da ake soke.

Ina cikin mutanen da aka zaba domin yin takara da Abiola - Boss Mustapha
Ina cikin mutanen da aka zaba domin yin takara da Abiola - Boss Mustapha

Mustapha ya bayyana wa duniya hakan ne a yayin da ya ke jawabin bude taron na musamman don karrama wadanda suka sami lambar girma ta kasa da aka gudanar a fadar Aso Villa dake Abuja. "Na shaidawa Ambasada Kingibe a dakin tattauna cewa za'a zabe ni a matsayin wanda zai yi takara da MKO."

KU KARANTA: Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

Mustapha ya cigaba da cewa, "har ma na kira shi a waya lokacin yana Saudiya kuma mun tattauna a kan batun."

Ya ce tabbas ranar 12 ga watan Yuni ranar ce mai muhimmanci a tarihin Najeriya wanda ke tunatar da mu irin gwagwarmayar da sauran yan Najeriya su kayi don ganin an kafa demokradiyya mai dorewa, kuma ranar an bude sabuwar shafi a tarihin siyasar Najeriya.

A cewar Mustapha, lambar girmar da aka baiwa jaruman zai tabbatar wa al'ummar Najeriya cewa gwamnati bata manta da gudunmawar da wadanda suka sami lambar yabon suka bawa Najeriya ba kuma alama ce da ke nuna gwamnatin Buhari tana mutunta demokradiyya.

Sakataren gwamnatin tarayyan kuma ya ce zaben na 12 ga watan Yunin 1993 shine zabe na farko da akayi inda yan Najeriya suka kada kuri'unsu ba tare da la'akari da bangarenci, yare ko kabila ba sai dai saboda amincewa da su kayi da dan takarar da kuma son cigaban Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel