Ina da shekara 13 akayi mani auren fari – Maryam Gidado
Shahararriyar jarumar nan da tauraronta ke hasanakawa a masana’antar Kannywood, Maryam Gidado wacce akafi sani da Maryam Babban ta yi tsokaci akan wani babi day a shafi rayuwarta.
A cewar Maryam ita bazawara ce domin ta taba yin aure har sau karo biyu. Jarumar ta bayyana cewa anyi mata auren fari tana da shekaru 13 a duniya kasancewarta Bafulatanar asali.
Ta kuma ta haifi ‘Yarta ta farko tana da shekaru 14 bayan shekara daya da aurar da ita ga mijin nata na fari.
Ta kuma kara yin aure inda anan ne ta haifi ‘Danta na biyu,sannan kuma ta bayyana cewa alokacin da take da cikin ‘Dan nata na biyu ne sai mijin ya gudu ya bar ta.
KU KARANTA KUMA: Kasar Ghana, da sauran kasashen Afrika zasu dunga siyan mai daga matatar Dangote
Daga karshe Maryam ta jaddada cewa burin ta ya cika a yanzu musamman a harkar fim sai dai kawai addu'an Allah ya bata miji nagari ta raya Sunnah.
A baya Legit.ng ka rahoto maku cewa jarumi Nuhu Abdullahi ya jaddada soyayyarsa ga Fati Washa harma yace shi a shirye yake ya aureta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng