Ina son Fati Washa kuma zan iya aurenta – Nuhu Abdullahi
Shahararren Jarumin nan na Kannywood, Nuhu Adullahi ya kasance daya daga cikin yan wasan da suka shiga farfajiyar shirya fina-finan da kafar dama.
Cikin dan kankanin lokaci da shigarsa harkar jarumin ya samu tarin daukaka da nasarori inda har yayiwa wasu da riga shi shiga harkar zarra.
A wata hira da jarumin yayi da jaridar Premium time ya bayyanawa duniya irin son da yake yiwa jaruma Fati Washa kuma har ya jaddada cewan shi zai iya auren ta.
Da aka tambaye shi jarumar da ta fib urge shi a masana’antar yace: “ Fati Washa a koda yaushe itace zabina bazanyi nadama ba inma furta cewa ina sonta.”
Jarumin ya kara da cewa ita din ta musamman ce,ta kasance tana kyautata min tabbas zan iya yin komai dan ganin nima na kyautata mata dan tana da saukin kai ga girmama manya.
KU KARANTA KUMA: Masu haya 5 sun lalata yar mai gidansu mai shekaru 12 tare da yi mata ciki
Jaridar ta kara yi masa tambaya da cewa meyasa ka zabi Fati Washa ita kadai acikin duk ‘Yan matan Industry,Sai yace “kamar yadda na gaya maka bazan iya bayyana maka yadda make jiba.
“Amma ina matukar mutunta ta duk da ina da kawaye irin su Rahama Sadau da sauran su."
Da aka tambaye shi ko zai iya auranta yace: “Tabbas in haka ta faru zanji dadi,in mutum ya kyautata maka zaifi kyau shima ka kyautata masa.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng