Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya isa Abuja bayan ziyarar da ya kai kasar Maroko
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Abuja a yammacin yau Litinin, 11 ga watan Yuni bayan ziyarar da ya kai kasar Moroko.
Hakan ya biyo bayan gayyatar da sarkin Morokon ya yi ma shugaba Buhari.
A taron da aka gudanar a Rabat, shugabannin biyu sun sake tabbatar da yarjejeniyar da suka kulla tsakanin Najeriya da Marokon, tare das a hannu a yarjejeniyar safari gas zuwa Afrika maso arewa ta hanyar tekun Atlantic.
Haka zalika, Sarki Mohammed ya yabama kokarin shugaba Buhari a kan rawar da yake takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar sa.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya sauka kasar Moroko, an masa tarbar girma (Hotuna)
Zaku tuna cewa an yi yarjejeniya tsakanin Najeriya da Maroko a watan Disamban 2016 domin farfado da masana’antun takin zamani. Zuwa yanzu an farfado da masana’antu 14.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng