Alkawari da cikawa: An gyara gadar Jebba-Mokwa da ta fado, amma na wucin gadi

Alkawari da cikawa: An gyara gadar Jebba-Mokwa da ta fado, amma na wucin gadi

- Hukumar tsare hadurra ta sanar da masu ababen hawa cunkoson da ke titin bayan faduwar gadar

- Titin Mokwa zuwa Jebba, wanda ya hada jihohin Niger da Kwara, Ita ce babbar hanya tsakanin Abuja da kuma yammacin kasar nan

- Cunkoson ababen hawan ya shafi dukkanin bangarorin titin kuma babu hanyar wucewa har sai ranar lahadi

Alkawari da cikawa: An gyara gadar Jebba-Mokwa da ta fado, amma na wucin gadi
Alkawari da cikawa: An gyara gadar Jebba-Mokwa da ta fado, amma na wucin gadi

An samu sassaucin cunkoson ababen haka sakamakon gyara na wucen gadi da aka yi wa gadar Mowo bayan faduwar da tayi a daren asabar.

Shawo kan matsalar da akayi na wucin gadi ya biyo baya ne kasa da awoyi ashirin da hudu bayan ministan aiyuka, Babatunde Fashola, ya tabbatar wa da masu ababen hawan da ke bin hanyar cewa za a Shawo kan matsalar.

Gadar Mowo na nan a kilometer 18 daga garin Mokwa a jihar Niger. Gadar na nan a kusa da gadar Tatabu, wacce ta fadi a 2017 kuma Gwamnatin Najeriya tayi gaggawar gyara ta.

Cunkoson ababen hawan ya shafi dukkanin bangarorin titin kuma babu hanyar wucewa har sai ranar lahadi.

Mai magana da yawun hukumar tsare hadurra, Bisi Kareem, ya shawarci masu ababen hawa da su bi titin lokoja a maimakon nan Idan zasu je Legas da Abuja.

Amma lokacin da majiyarmu ta ziyarci gurin gadar a ranar litinin, ta tarar babu cunkoson.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, gurin da ya fadin an cike shi da duwatsu da kasa, yanda masu ababen hawan zasu samu damar wucewa lafiya lau.

Umar Umaru, wani mai abun hawa yace, anyi gida ta wucin gadi da gaggawa.

DUBA WANNAN: Ma'aikacin banki ya saci N3m

Legit.ng ta lura cewa akwai jami'an hukumar tsare haddurra a gadar, suna lura da bada hannu ga masu ababen hawa.

Masu ababen hawa sunyi jinjina ga Gwamnatin sakamakon taimakon gaggawa da ta bada.

Har yanzu dai bamu tabbatar da cewa za a cigaba da aikin gyaran gadar ba don duk wani yunkuri da wakilinmu yayi don zantawa da jami'an hukumar tsare haddurran bai yuwu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng