Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna

Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna

Dakarun rundunar Sojin Kasa sun yi ma gungun masu garkuwa da mutane diran mikiya a yankin karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda suka karkashesu kisan kiyashi, tare da kwato babura 36 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin rundunar, Birgediya Texas Chukwu ne ya sanar da haka, inda yace Sojojin sun kashe yan bindigan ne a ranar Asabar, 9 ga watan Yuni, a yayin aikin tsaro na musamman mai taken ‘Operation idon raini’.

KU KARANTA: Jami’an Sojojin Najeriya sun kubutar da wasu mutane daga hannun barayin mutane a Kaduna

Sanarwar ta bayyana cewar Sojoji sun kashe yan bindiga a kauyen Dogon Dawa, a lokacin da suka dira kasuwar hatsi dake kauyen da nufin satar kayan abinci, sa’annan sun kwato wayoyin salula guda biyar tare da kudi Naira 19, 135.

Dakarun Sojin Najeriya sun yi ma masu garkuwa da mutane kisan kiyashi a Kaduna
Dakarun Sojin Najeriya

Haka zalika Sojojin sun cafke wani mutumi mai suna Abdulkadir Samaila da wani Alhaji Yahaya, wadanda ake zarginsu da zama yan aiken masu garkuwan, suna kai musu kayan aiki da suka hada da makamai da kuma yi tattaro musu bayanan sirri.

Da bincike ya tsananta akan mutanen biyu, Sojoji sun binciko tarin abubuwa daga hannunsu, da suka hada da Mota kirar Opel, wayoyin Salula guda biyu da zambar kudi naira 34,000.

A wani labarin kuma, Sojoji sun yi artabu da yan bindiga a kauyen Sabon Fili, inda suka hallaka guda uku daga cikinsu, kuma suka kwato wayoyin salula guda hudu, babura hudu da kayan shaye shaye.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng