Da dumin sa: jirgin shugaba Buhari ya tashi zuwa kasar Morocco
Da ranar yau, Lahadi, 10 ga watan Yuni, jirgin shugaba Buhari ya tashi ya zuwa birnin Rabat na kasar Morocco a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da zai yi a kasar. Tun a jiya ne fadar shugabn kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari zai bar Najeriya a yau, Lahadi, zuwa kasar Morocco.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari zai tafi Maroko ne bisa gayyatar mai martaba sarkin Maroko, King Mohammed VI, domin tattaunawa kan tattalin arzikin kasashen biyu da suka fara yayinda sarkin ya kawo ziyara Najeriya a Disamban 2016.
DUBA WANNAN: 'Yan nPDP sun gindaya sabbin sharadi kafin komawa teburin sulhu da APC
Jawabin yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiyan kwana 2 masarautar Maroko ranan Lahadi. Zai tafi tare da gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, da gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru da wasu manyan jami’an gwamnati.”
“Zaku tuna cewa an yi yarjejeniya tsakanin Najeriya da Maroko a watan Disamban 2016 domin farfado da masana’antun takin zamani. Zuwa yanzu an farfado da masana’antu 14.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng