Kotu ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane 5 da suka kashe makiyaya a Yola

Kotu ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane 5 da suka kashe makiyaya a Yola

Wata babban kotu a Yola karkashin Justis Abdul-Azeez Waziri ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane biyar da aka samu da laifin kissan gilla tare da kashe wani makiyayi.

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Alex Amos da Alheri Phanuel da Holy Boniface da jerry Gideon da Jari Sabagi wadanda ke zaune a karamar hukumar Demsa a jihar Adawama.

An same su da laifin hadin baki tare da aikata kissan gilla wanda ya sabawa sashi na 96(1) (a) da sashi na 79 da 221 (b) na Penal Code na Jihar Adamawa ta shekarar 1997.

Kotu ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane 5 da suka kashe makiyaya a Yola
Kotu ta zartas da hukuncin kisa a kan wasu mutane 5 da suka kashe makiyaya a Yola

KU KARANTA: Za mu fice daga jam'iyyar APC - Nyako

Wadanda aka yanke wa hukuncin sun aikata laifin ne a ranar 1 ga watan Yunin 2017 a kauyen Kadamun da ke karamar hukumar Demsa inda da gangan suka hada baki suka kaiwa makiyaya uku hari inda suka kashe guda daya, Adamu Buba kuma suka jefa gawarsa a rafi sannan suka yiwa shanu da yawa rauni.

Justis Waziri ya ce Lauya mai shigar da kara Salihu Mohammed ya gabatar da dalilai da shedu da suka gamsar da kotun cewa wadanda ake tuhuma da laifin sun aikata laifin.

Hakan yasa Alkalin ya yanke musu hukuncin kisa ta hnayar rataya tare da zaman gidan kurkuku na shekaru uku wanda za'a zartas a tare.

Sai dai Alkalin ya kara da cewa, "wadanda aka yanke wa hukuncin suna da ikon daukaka kara a kotun daukaka kara a jihar Yola cikin kwanaki 90 daga ranar da aka yanke musu hukuncin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel