Wani Mutum ya Kashe Kansa a Masallacin Harami na Birnin Makkah

Wani Mutum ya Kashe Kansa a Masallacin Harami na Birnin Makkah

Cikin wani rahoto mai kunshe da ban al'ajabi ya bayyana cewa, wani matashin mutum ya kashe kansa yayin da ya jefo kansa tun daga saman bene na kololuwa dake babban Masallaci mai alfarma na Birnin Makkah a can Kasar Saudiyya.

Hukumomin tsaro na Kasar Saudiyya sun bayyana cewa, wannan matashin mutum da ya ziyarci kasa mai tsarki domin gudanar da aikin Umarah a wannan wata na Ramadana ya mutu ne nan take yayin da ya fado kasa da misalin karfe 9.20 na daren ranar Juma'ar da ta gabata.

Jami'an tsaro yayin yiwa masu dawafi shinge da kare su wajen kaiwa ga Matashin
Jami'an tsaro yayin yiwa masu dawafi shinge da kare su wajen kaiwa ga Matashin

Ma'aikata yayin kai dauki ga wannan Matashi
Ma'aikata yayin kai dauki ga wannan Matashi

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan matashi bai wuci shekaru 26 a duniya ba kuma dan asalin kasar Faransa ne da ya yi tsarki na shiga addinin Islama kamar yadda wata jarida ta kasar Taki, Daily Sabah ta bayyana.

KARANTA KUMA: Rushewar wani Gini ta salwantar da Rayuka 3 da raunata Mutane 7 a Garin Zaria

Legit.ng kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, wannan ba shine karo na farko da wani mahaluki ya yi yunkurin kashe kansa a harabar Masallaci mai Alfarma daura da Dakin Ka'aba duk da cewar kisan kai a addinin Islama yana daya daga cikin manyan laifuka na kololuwa da ba bu yafiya ga duk wanda ya aikata hakan.

An garzaya da gawar wannan Matashi zuwa asibiti domin binkicen dalilin da ya sanya ya yankewa kansa wannan mummunan hukunci tare da binciken yadda ya aikata hakan.

A shekarar da ta gabata ne wani mutum dan kasar ta Saudiyya ya yukurin kashe kansa ta hanyar bankawa kansa wuta a gaban dakin Ka'aba yayin da jami'an tsaro suka yi gaggawar hana shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng