Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari

Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abunda ya tattaunawa a ganawar da yayi da wasu yan wasa a fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya gana da su Ali jita, Yakubu Muhammed, Tobi Bakare na Big Brother, Smal Doctor da sauransu.

Buhari ya tabbatar da ganawar tasu a shafinsa na Twitter.

Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari
Abunda na fadama su Ali Jita da sauran matasa da suka kawo mun ziyara – Shugaba Buhari

Ya bayyana cewa a lokacin ganawarsu ya baasu tabbaccin yin duk wani kokari da zai basu damar ganin cigaba a harkokinsu na nishadantarwa dama ganin matasa sun inganta.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin kungiyar yakin neman zaben sa (hotuna)

Ya kuma bukaci matasan Najeriya da su mallaki katin zabe sannan su yi zabi nagari a 2019.

Ya kuma jadadda masu cewar su zabi duk dan takarar da yayi masu , domin hakan shine yancin damokradiyya. Haka zalika ya bayyana masu cewa katin zabensu yancin su ne kuma kada suyi la’akari da kabilanci ko addini.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel