Aleppo, Latakiyyah da sauran Birane mafi tsufa a tarihin Duniya

Aleppo, Latakiyyah da sauran Birane mafi tsufa a tarihin Duniya

Mun shiga littatafan Tarihi na Duniya a wannan karo inda mu ka kawo maku Garuruwan da su ka fi kowane tsufa a Duniya. Bangaren binciken tarihi na Kungiyar UNESCO ta yi wannan nazari.

Aleppo, Latakiyyah da sauran Birane mafi tsufa a tarihin Duniya
Birnin Alesandiriya da ke Afrika tsohon Gari ne inji Masana

UNESCO Kungiya ce ta Majalisar dinkin Duniya da ke binciken ilmin kimiyya da fasaha da kuma al’adun Kasashen Duniya domin hada-kan alumma. A binciken da aka yi, manyan Biranen da su ka fi dadewa su ne:

1. Alefo

Birnin Aleppo wanda shi ne babban Birnin Kasar Siriya ya fi shekaru 12000 da kafuwa a Duniya inji Masana tarihi.

KU KARANTA: Wata yarinya ta kashe jaririnta a Jihar Sokoto

2. Jeriko

Garin Jeriko da ke cikin Kasar Falastina ma dai ya fi shekaru 10000 da kafuwa inji wadanda su ka san tarihin Duniya.

3. Damashk

Garin da Turawa ke kira Damascus ya fi shekaru 9000 a Duniya. A lokacin da Damashk na Kasar Sham wanda yanzu ta ke Siriya.

4. Alesandiriya

Bincike ya nuna cewa Birnin Alesandiriya da ke Kasar Misra a cikin Arewacin Afrika tsohon Gari ne wanda kusan shekarun sa 8000.

5. Latakiyya

A kasar Siriya wanda ta ke Sham a da ne dai Birnin Latakiyyah ta ke. Garin ya fi shekaru 7000 a tsaye inji Masana.

Irin su Birnin Sana’a da ke Kasar Yemen da su Birnin Khurasan na Kasar Afghanistan da kuma Birnin Raqqah da ke Kasar ta Siriya ma dai sun dade da kafuwa kamar yadda bincike ya nuna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng