Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara

Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara

- Dakarun soji sunyi wa yan bindiga kaca-kaca a wasu kauyukan Zamfara

- Sojin sun kai samamen ne sakamakon bayanan sirri da suka samu a kan ayyukan yan bindigan

- Sojin sun halaka yan bindiga guda biyar tare da kwato wasu kayayaki a sansanin yan bindigan

Dakarun sojin Najeriya na bataliyar 223 karkashin atisayen Operation Idon Raini sun kai wata samame a Danguru da kuma dajin Babandoka da ke yankin Dansadau a karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.

Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara
Dakarun soji sunyi wa 'yan bindiga diran mikiya a Zamfara

Sojin sunyi nasarar halaka yan bindiga uku a harin da suka kai musu a mabuyarsu a ranar 6 ga watan Yunin 2018 tare da lalata kayayakinsu.

KU KARANTA: Soja mazan fama: Wani jarumin soja ya kwace bindiga daga hannun 'dan fashi da makami

A wata samamen mai kama da wannan, Sojin sun ziyarci kauyukan Gobirawa da Kwacha da ke kusa da dajin Madaka duk dai a yankin Dansadau da ke karamar hukumar Maru da ke jiha Zamfara.

Sojin sun halaka yan bindiga guda biyu yayin da saura suka tsere da raunuka sakamakon luguden wutan da sojojin su kayi musu.

A halin yanzu, hukumar sojin ta bazama don kamo wadanda suka guda yayin da aka kai musu samamen.

Kayayakin da sojojin suka kwato sun hada da babur guda daya da wayar salula guda daya.

Hukumar sojin na kira ga al'umma suyi gagawan sanar da jami'an tsaro duk wani abin da ke faruwa a unguwaninsu da basu amince dashi ba saboda a dauki mataki cikin gagawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel