Mutane 6 sun fada tarkon 'Yan sanda dauke da dauri 211 na Tabar Wiwi a Jihar Sakkwato

Mutane 6 sun fada tarkon 'Yan sanda dauke da dauri 211 na Tabar Wiwi a Jihar Sakkwato

Wani sabon rahoton da sanadin shafin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa, hukumar 'yan sanda ta samu nasarar cafke wasu mutane shidda bisa aikata laifin mallaka da fataucin Tabar wiwi a jihar Sakkwato.

Hukumar ta samu nasarar cafke wannan baragurbin mutane uku a tsohon filin Jirgin Sama na jihar Sakkawato da suka hadar da; Faruku Buda, Nura Isah da kuma Mainasara Muhammad.

Baya ga haka kuma hukumar ta cafke masu samar da Tabar wiwin da suka hadar da; Denis Okpovoka, Francis Henry da Ovia Ochuko wanda dukkanin su mazauna kauyen Raymond ne a jihar Sakkwato.

Mutane 6 sun fada tarkon 'Yan sanda tare da Tabar Wiwi a Jihar Sakkwato
Mutane 6 sun fada tarkon 'Yan sanda tare da Tabar Wiwi a Jihar Sakkwato

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Cordelia Nwawe, shine ya bayyana hakan da cewar cikin wani sintiri da jami'an tsaro suka gudanar da misalin karfe 2.30 na ranar 26 ga watan Mayu, hukumar ta samu nasarar cafke wannan miyagun mutane tare da dauri 211 na ganyen wiwi.

KARANTA KUMA: Kashe-Kashen Makiyaya: Kungiyar Miyetti Allah ta yi Barazanar shigar da 'Karar 'Yan Jarida masu 'Kage

A yayin gudanar da wani sintirin a ranar 27 ga watan Mayu, hukumar ta yi ram da wani kaso na mutane uku masu cinikayyar Tabar Wiwi a sakamakon rahoton da mutane farko suka baiwa jami'an yayin da suka ji uwar bari.

Legit.ng ta fahimci cewa, a halin yanzu hukumar 'yan sandan na Birnin Shehu ta ci gaba da gudanar da bincike na diddigi domin gano dukkanin masu hannu cikin wannan sana'a ta fataucin kayan maye.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng