Diyar Marigayi Sheikh Jafar ta haifawa Mahaifin ta Takwara

Diyar Marigayi Sheikh Jafar ta haifawa Mahaifin ta Takwara

- An yi wa Marigayi babban Malamin Musulunci Ja’afar Takwara

- ‘Diyar Shehin Malamin ta haifi Yaro da aka sa wa suna Ja’afar

- Ana dai sa rai wannan yaro ya gaji Iyayen sa wajen karantarwa

A watan nan na Azumin Ramadan ne mu ka samu labari cewa ‘Diyar babban Malamin addinin Musuluncin nan da aka yi a Arewacin Najeriya watau Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ta samu haihuwar yaro namiji.

A karshen watan Mayu ne Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta sanar da cewa an samawa Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam jika wanda kuma aka yi masa takwara da shi aka radawa yaron suna Ja’afar Ibn Ibrahim Ibn Abdullahi.

KU KARANTA: Malamin Addini yayi kira a saki El-Zakzaky

Zainab Ja’afar Mahmud Adam wanda ita ce babbar ‘Diyar bajimin Malamin ta haifi yaro wanda ake sa rai zai gaji Iyayen sa da kakanin sa. A Ranar 25 ga Watan Mayu ne Hajiya Zainab ta sauke yaro tsalele da aka sa wa Ja’afar kamar dai Kakan sa.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Kungiyar Izala ta Musulunci a tsakiyar azumin nan, Mai jegon watau ‘Diyar wannan babban Malami masanin Al-Kur’ani ta sauka lafiya, haka ma kuma Mijin ta Dr. Ibrahim Abdullahi Rijiyar Lemo yana nan kalau.

Manyan Malaman addinin Musulunci tuni su ka yi wa wannan yaro ‘dan gidan Malamai addu’ar ya gaji Kakan sa wanda aka kashe a 2007 yana limancin sallar asuba a cikin Garin Kano.Mahaifin wannan yaro dai shi ma 'Dan gidan manyan Malamai ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel