Dandalin Kannywood: Abinda Saraki yace game da 'yan fim din Hausa
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yaba wa yan fim din Hausa da manya - manyan jiga-jigan masana'antar fim din wadanda aka fi sani da Kannywood sakamakon gudumawar da suke badawa ta fannin raya al'adun Hausa, da kuma samar da aiyuka ga dubunnan mutane a fadin kasar nan
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yaba wa yan fim din Hausa da manya - manyan jiga-jigan masana'antar fim din wadanda aka fi sani da Kannywood sakamakon gudumawar da suke badawa ta fannin raya al'adun Hausa, da kuma samar da aiyuka ga dubunnan mutane a fadin kasar nan.
DUBA WANNAN: Wata mahaukaciyar guguwa tayi sanadiyyar asarar gidaje sama da 1,000 a wata jiha a arewacin Najeriya
Saraki ya yabawa 'yan fim dinne yayin da ya karbe su lokacin da suka kai masa ziyara a jiya.
Shugaban majalisar ya sa hotunan shi tare da 'yan fim din Hausan a shafin sa na instagram a ranar Larabar nan. Saraki ya yabawa masana'antar fim din inda yace, "Yan fim din mu na gida Najeriya sune suke na biyu a dukkanin masana'antun fim na duniya".
Wannan ne yasa, ganawa mazan su da matan su, da masu bada umarni, da masu shirya shirye shiryen su a daren jiya ya zamo min abin farinciki. Salisu Aliyu(Chali), Ali Nuhu, Tijjani Faraga da Maryam Habila su suka jagorance su.
Ya kara da cewa wadannan mutane suna iya bakin kokarin su don habaka harshen hausa a sinima wanda miliyoyin mutane ke kallo.
"Masana'antar Kannywood ta samar da aikin yi ga miliyoyin matasa ta hanyar kayatarwa da nishadantarwa," inji Saraki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng