A nuna mani aiki 1 da Buhari ya kammala a shekaru uku — Tanko Yakasai
Babban jigon arewa kuma shugaban kungiyar dattawan Arewa, Alhaji Tanko Yakasai ya bukaci a nuna masa wani aiki daya da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala a shekaru uku da ya kwashe akan karagar mulki.
Ya kuma nemi sanin adadin mutanen da aka yankewa hukunci akan tuhumar rashawa a shirin yaki da rashawan da shugaban kasar ya kaddamar.
Yakasai yayi zargin cewa har yanzu Buhari ya gaza hukunta tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda aka kama dumu-dumu da laifin rashawa.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tanko Yakasai ya bayyana dattawan Arewa basu tsayar da ko wani dan takara ba tukuna a tsakanin jam’iyyun APC da PDP a 2019.
Yakasai ya bayyana cewa tsayarwarsu zai kasance akan manufofin yan takara ba wai sanayar halayensu ba,” jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: 2019: Abunda Arewa zata duba wajen marawa yan takarar shugaban kasa baya - Yakasai
Yakasai ya bayyana cewa a baya Yan Najeriya sunyi kuskure, daga tsohon shugaban kasa Olusegun zuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen zabar hallaya ba wai ingancin shirye-shiryen da yan takarar suka tanadar ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng