Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka sanatocin Najeriya kyalkyalewa da dariya

Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka sanatocin Najeriya kyalkyalewa da dariya

Sanatocin Najeriya sun kyalkyale da dariya bayan shugaban majalisar dattijai, Abubakar Bukola Saraki, ya ambaci Kalmar “transmission” a cikin wasikar da shugaba Buhari ya aike masu.

Saraki ne ya fara barkewa da dariya a daidai lokacin da ya zo kan Kalmar ta “transmission’’ a yayin da yake karanta wasikar shugaba Buhari ga ragowar ‘yan majalisar ta dattijai.

Saboda kyakyacewa da dariya, saida Saraki ya sake fara karanto wasikar tun daga farko.

Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka sanatocin Najeriya kyalkyalewa da dariya
Wata kalma cikin wasikar Buhari ta saka sanatocin Najeriya kyalkyalewa da dariya

Kalmar “transmission” ta shiga bakin ‘yan Najeriya tun bayan nuna wani faifan bidiyo na shugaban rundunar ‘yan sanda, Ibrahim Idris, yana inda-indar karanta Kalmar yayin karanta wani jawabi.

Tun a farkon ballewar faifan bidiyon a dandalin sada zumunta, hukumar ‘yan sanda ta zargi majalisar dattijai da kitsa makirci domin tozarta sifeto Idris.

DUBA WANNAN: Zan tabbatar an garkame Oyegun a gidan yari - Rochas

Har yanzu ana cigaba da nuna yatsa tsakanin sifeton ‘yan sanda da Bukola Saraki. Ko a yau hukumar ta ‘yan sanda ta bayyana cewar gayyatar da ta yiwa Saraki domin kare kan sa a kan batun fashin garin Offa na nan daram bayan a baya hukumar ta bayyana janye gayyatar.

Hukumar ‘yan sanda t ace ta kara samun wasu sabbin shaidu dake kara nuna hannun Saraki cikin fashin da aka yiwa bankuna 5 a garin Offa na jihar Kwara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng