Mutane 189 sun yi nasarar Jarrabawar shiga Aikin 'Yan sanda a jihar Jigawa

Mutane 189 sun yi nasarar Jarrabawar shiga Aikin 'Yan sanda a jihar Jigawa

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta Najeriya ta bayyana sakamakon wata jiha daga cikin Jihohin Arewa na wadanda suka zana jarrbawar tantance shiga aikin na hukumar 'yan sanda.

Hukumar 'yan sandan reshen jihar Jigawa ta bayyana cewa, mutane 189 sun samu nasara cikin 1, 728 da suka zana jarrabawar tantancewa wajen neman shiga aikin 'yan sanda.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a babban Birni na Dutse a ranar Larabar da ta gabata.

Mutane 189 sun yi nasarar Jarrabawar shiga Aikin 'Yan sanda a jihar Jigawa
Mutane 189 sun yi nasarar Jarrabawar shiga Aikin 'Yan sanda a jihar Jigawa

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar gudanar da jarrabawar tantance manema shiga makarantun gaba da Sakandire ta JAMB ita ta dauki nauyin gudanar da wannan jarrabawa cikin fadin kasar nan a ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata.

Jinjiri yake cewa, an gudanar da wannan jarrabawa ga manema shiga aikin dan sanda cikin shiyoyi shidda a fadin Jihar ta Jigawa.

KARANTA KUMA: 'Yan Majalisar Wakilai Baballe da Chika sun bayyana Kutungwilar da ta sanya aka gudanar da Zaman Majalisar Dokoki ta Tarayya

Cikin adadin mutane 1, 728 da suka zana jarrabawar guda 189 ne kacal suka samu nasara wanda aka fitar da jerin sunayen su domin sake tatance su a mataki na gaba inda za a kuma a duba lafiyar su kamar yadda SP Jinjiri ya bayyana.

Legit.ng ta fahimci cewa, kimanin mutane 4, 705 ne suka nemi shiga aikin na 'yan sanda a fadin jihar ta Jigawa a sakamakon lamunin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar na daukar sabbin ma'aikata 6,000 na hukumar a fadin kasar baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel