2019: Zan sake yin takarar gwamna a jihar Taraba - Mama Taraba
- Ministan harkokin mata Aisha Alhassan ta bayyana niyar ta na sake fitowa takarar gwamna a jihar Taraba
- Alhassan wanda ake yiwa lakabi ta 'Mama Taraba' ta bayyana hakan ne a sakatariyar APC a Abuja bayan kammala nadin sabbin ciyamomi a jiya
- Mama Taraba ta ce Allah ne ke bayar da mulki kuma za ta cigaba da Imani da shi tare da kusanci da talakawan Taraba
Ministan harkokin mata na kasa, Senata Aisha Alhassan ta bayyana niyyar ta na sake tsayawa takara a babban zaben 2019 da ke zuwa.
Sanatan wanda aka fi sani da 'Mama Taraba' ta fadi hakan ne a jiya Talata a sakatariyar jam'iyyar APC a Abuja bayan an kammala taron rantsar da sabbin ciyamomin jam'iyyar guda 35.
KU KARANTA: Kishi ya saka wata mata yi wa kishiyar ta wanka da tafasashen ruwa
Alhassan ta ce kowa ya sani cewa ita ta lashe zaben gwamna a shekarar 2015 a jihar Taraba, har ma da yan jam'iyyar PDP, kuma ta kara da cewa za ta sake fitowa takarar idan Allah ya yi mata tsawon rai.
"Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so. Na yi nasara a 2015 amma Allah bai bani mulkin ba. Zan cigaba da imani da Allah tare da talakawan jihar Taraba kuma cikin ikon Allah zanyi nasaram," inji Alhassan.
Kazalika, ta kuma bayar da tabbacin cewa sabon ciyaman din jam'iyyar APC na jihar Taraba zai hada karfi da karfe tare da wadanda su kayi takara dashi don ganin cewa jam'iyyar ta cigaba da zama tsintsiya madaurin ki daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng