'Yan Majalisar Wakilai Baballe da Chika sun bayyana Kutungwilar da ta sanya aka gudanar da Zaman Majalisar Dokoki ta Tarayya

'Yan Majalisar Wakilai Baballe da Chika sun bayyana Kutungwilar da ta sanya aka gudanar da Zaman Majalisar Dokoki ta Tarayya

Wasu 'Yan Majalisar Wakilai Biyu, Bashir Baballe da Abubakar Chika, sun bayyana kutungwilar da ta sanya Majalisar Dattawa ta garazayo Majalisar Wakilai domin gudanar da Zaman majalisar Dokoki ta kasa baki daya a lokaci guda.

'Yana Majalisar biyu sun bayyana cewa, zaman Majalisar dokoki na tarayya da aka gudanar ba ya da wata manufa ta ababen da suka shafi Kasar nan ta Najeriya face manufa da ta shafi shugabannin Majalisar.

A yayin ganawa da manema labarai na jaridar Daily Nigerian a wayar tarho, Mista Baballe da yake wakilicin Kananan hukumomin Ungogo da Minjibir na Mazabun Jihar Kano ya bayyana cewa, yayi mamakin yadda ba a tashi kiran zaman Majalisar Dokoki ta kasa ba sai yanzu da aka rage jami'an tsaro masu kare shugaban Majalisar dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai.

A kalamansa, "akwai babbar damuwa yayin da ake faman zubar da jinin Mutane a kasar nan, shugabannin Majalisar Dokoki ta Kasa ba su nemi a gudanar da wani zama dangane da lamarin ba, sai yanzu da aka rage yawan jami'an tsaro dake kare Saraki da Dogara kwanaki kadan da suka gabata."

Bashir Baballe
Bashir Baballe

"Karo na karshe da aka gudanar da zaman Majalisun biyu lokaci guda shine yayin da 'Yan Baranda suka kai hari na sace Sandar girma ta Majalisar Dattawa. Amma ba bu wani zama da aka gudanar yayin da ake kai hare-hare kan al'ummomi daban-daban a kasar ana zubar da jinin su ba tare da hakki ba."

Yake cewa, "sun gudanar da wannan zaman ne kadai domin kitsa wani tuggu da cimma manufa ta Kutungwila."

"Dangane da tozarci, wane laifi Sanata Ali Ndume da 'Dan Majalisar Wakilai Abdulmumin Jibrin suka aikata da har aka kunyata su kuma shugabannin Majalisun suka dakatar da su har na tsawon wasu lokuta?"

KARANTA KUMA: Kasar Jamus za ta Yaso 'Yan Najeriya 30, 000 da suka yi Gudun Hijira

'Dan Majalisa Baballe ya kuma kalubalanci yadda Majalisar Dokoki ta Kasa ta juya bayan ta akan akidar shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta yakar cin hanci da rashawa a kasar nan, inda ya jaddada cewa "duk wani dan majalisa da ake tuhuma yaje ya wanke kansa muddin yana da gaskiya a madadin ya fara zargin ba ai masa adalci ba."

'Dan Majalisa Abubakar Chika, mai wakilcin kananan hukumomin Shiroro, Rafi da Munya cikin Mazabun jihar Neja, ya goyi bayan babatun Bashir Baballe inda yake cewa ya kamata Majalisar Dokoki ta tashi ta farka domin sanin nauyin da rataya a wuyan ta.

Ya kuma kalubalanci yadda wasu daidaikun 'yan Majalisa ke yunkurin juya bayan su akan Sufeto Janar na 'Yan sanda, Ibrahim K. Idris.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng