Waka a bakin mai ita: Jawabin ‘yan fashin Offa da ya saka Saraki cikin tsaka mai wuya
Hukumar ‘yan sanda ta saki jawabin ‘yan fashin da suka tafka barna a garin Offa ranar 5 ga watan afrilu da kuma suka shaidawa ‘yan sandan cewar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, na daga cikin masu daukan nauyin su.
Ga jawabin ‘yan fashin da suka yiwa jami’an ‘yan sanda kamar yadda jaridar Thisday ta wallafa.
Wani daga cikin ‘yan fashin da ake kira AY kuma shugaban wata kungiya Liberation Youth Movement dake kudancin jihar ya shaidawa ‘yan sandan cewar, “muna da alaka da shugaban majalisar dattijai domin mu yaran sa ne. Muna nan a kowanne bangare na jihar Kwara kuma mun dade muna yi masa aiki tun yana jam’iyyar PDP.”
Da hukumar ‘yan sanda ta tambaye shi ko wane irin aiki suke yiwa Saraki, sai AY y ace, “mune ke yi masa bangar siyasa musamman a wuraren da muka ga alamun ba zamu samu nasarar zabe ba.”
DUBA WANNAN: Masu bawa Buhari shawara jahilai ne - Sheikh Gumi
Hukumar ‘yan sanda ta kara tambayar sa ko ta ya ya ne Saraki keda alaka ga aiyukan fashi da ku ke yi, sai y ace, “Saraki ne ke tsara mana duk abinda zamu yi domin hatta motar da muka yi amfani da ita wajen fashin, gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, da umarnin Saraki.”
Da hukumar ‘yan sanda ta kara tambayar sa ko Saraki na da masaniyar zasu aikata fashi, sai AY ya ce, alakar Saraki da fashin it ace, shine ya basu motar da suka yi amfani da ita kuma su yaran Saraki da gwamna Ahmed ne dake zaman ‘yan dabar su na siyasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng