Dan sandan da ya yi harbi tare da raunata mutane 4 a wurin taron APC a jihar Ekiti ya rasa aikin sa

Dan sandan da ya yi harbi tare da raunata mutane 4 a wurin taron APC a jihar Ekiti ya rasa aikin sa

Dan sandan da ya yi harbi a wurin taron yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Ekiti a jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, tare da raunata mutane 4 da suka hada da tsohon mamba a majalisar wakilai, Michael Opeyemi Bamidele, ya rasa aikin sa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, Mista Bello Ahmed, ya sanar da batun korar dan sandan daga aiki yayin wata hira da shi a wani shirin gidan Talabijin da aka nuna kai tsaye a Ado Ekiti, jiya.

Dan sandan da ya yi harbi tare da raunata mutane 4 a wurin taron APC a jihar Ekiti ya rasa aikin sa
Dan takarar APC a jihar Ekiti; Kayode Fayemi

Kazalika, kwamishinan ya gargadi ‘yan siyasa da su kasance masu biyayya da doka da kuma kiayaye duk wani abu da kan iya kawo rikici ko tayar da hankulan jama’a tare da bayyana cewar hukumar ‘yan sanda ba zata zuba ta na kallo ta bari ake karya doka da sunan yakin neman zabe ba.

DUBA WANNAN: An janye jami'an tsaron Saraki da Dogara

Mista Ahmed ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda zasu cigaba da yin aikin sub a tare da daukan bangare ko nuna wariya ba.

A ranar juma’a da ta gabata ne wani dan sanda ya yi harbi a wurin taron gangami da jam’iyyar APC ta shirya a jihar Ekiti domin kaddamar dad an takarar tan a gwamna, Kayode Fayemi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng