Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci tayi dukkan mai yiwuwa don ceto Leah Sharibu - Oloyode

Majalisar koli ta harkokin addinin musulunci tayi dukkan mai yiwuwa don ceto Leah Sharibu - Oloyode

Sakatare Janar na kwamitin koli ta harkokin addinin musulunci na Najeriya (NSCIA), Farfesa Ishaq Oloyede ya yi korafi kan yadda wasu ke amfani da Leah Sharibu 'yar makarantar Dapchi da 'yan Boko Haram suke garkuwa da ita don cinma manufar siyasarsu.

Oloyede ya ce garkuwa da Leah da sauran 'yan mata, musulmi da kirista da kungiyar Boko Haram ta yi abu ne da ke damun dukkan wadandan suka san ya kamata.

Kwamitin koli na musulunci ta sanya baki kan ceto Leah Sharibu - Oloyode
Kwamitin koli na musulunci ta sanya baki kan ceto Leah Sharibu - Oloyode

Ya ce shugabanin kungiyar ta NSCIA da ke wakiltan musulmin Najeriya sunyi amfani da dukkan hanyoyin da ya dace don ganin cewa anyi wa mayakan kungiyar ta Boko Haram afuwa muddin za su sako Leah da sauran yan matan da ke hannunsu kuma su ajiye makamansu.

KU KARANTA: Abin mamaki: An haifi wani jariri dauke da Kur'ani da carbi a jihar Bauchi, kalli hotuna

Oloyode ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke gabatar da wata kasida mai taken "Yadda za'a samar da zaman lafiya da shugabanci na gari a kasa mai addinai da kabilai daban-daban a mahangar addinin musulunci" wanda Right Development Limited masu wallafa jaridar Point Newspapers suka shirya a Legas.

Farfesan ya yi tsokaci kan kalaman da kungiyar kirista CAN ta furta na cewa za'a yi yakin addini muddin Leah Sharibu da ta ki karbar addinin musulunci ta mutu a hannun yan ta'addan.

Oloyode ya yi tsokaci kan rikicin da afkuwa tsakanin kabilun Tiv da Fulani a jihar Benue da kuma rikicin yan kungiyar Boko Haram kuma ya ce ba su da alaka da addinin bugu da kari ba dai-dai bane a rika zargin shugaba Muhammadu Buhari da hannu cikin asasa rikicin.

Ya ce wadannan rikice-rikicen sun dade suna faruwa tun kafin zuwan gwamnatin Buhari kuma al'ummar musulmi basu zargi gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da kitsa fitinar ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel