An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci

An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci

- An fara bawa jami'an 'yan sanda wata horo na musamman kan dabarun yaki da ta'addanci

- A kalla 'Yan sanda 150 ne daga jihohin Kano da Katsina da Jigawa ne za su samu wannan horaswan ta musamman

- Hukumar 'Yan sandan ta dauki wannan mataki ne saboda shirya jami'an ta fuskantar kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar

A kalla jami'an 'Yan sanda 150 ne daga jihohin Kano, Jigawa da Katsina ke samun horo na musamman a kan sabbin dabarun yaki da ta'addanci da ake gudanarwa a jihar Kano.

An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci
An fara bawa jami'an 'Yan sanda 150 horo ta musamman kan yaki da ta'addanci

An zabo jami'an Yan sanda masu mukamin DSP zuwa CSP daga rundunar hukumar na jihohin Kano, Jigawa da Katsina don basu wannan horon.

KU KARANTA: Wata ma'aikaciyar gwamnati ta rasa aikinta bayan sukar Osinbajo da Aisha Buhari

A yayin da ya ke bude taron a jiya, Sifetan Yan sanda na kasa IGP Ibrahim Idris ya ce an shirya horaswan ne saboda a habbaka ayyukan jami'an don fuskantar sabbin kalubalen tsaro da ke adabar kasar.

Sufeta Idris Ibrahim wanda ya samu wakilcin mataimakin sufeta Janar na hukumar mai kula da zone 1, AIG Dan Bature, ya kuma zaburar da mahalarta taron su mayar da hankali wajen dukkan horon da za'a basu domin ya kasance ba'ayi asarar kudaden da aka kashe wajen shirya horaswan ba.

Sauran hukumomin tsaro da suka samu hallartan taron sun hada da Hukumae Sojin Najeriya, Hukumar Sojin Sama, 'Yan sandan farar hula DSS, Hukumar Kula da fursunoni na kasa da kuma Hukumar tsaro da NSCDC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164