Gwamnan Gombe ya nemawa wata Baiwar Allah da aka kora daga aiki afuwa wajen Buhari
A karshen makon nan ne mu ka ji cewa wata Baiwar Allah mai suna Bolouere Opukiri ta rasa aikin ta a Gwamnatin Tarayya saboda sukar Matar Shugaban Kasa Aisha Buhari da Mataimakin Shugaban kasar Yemi Osinbajo.
Gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya roki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a dawo da wannan mata aikin ta. An dai sallami Opukiri daga aiki ne kan sukar da ta yi Farfesa Yemi Osinbajo a shafin ta na Tuwita.
Bolouere Opukiri ta Mataimakin Shugaban kasa Osinbajo bai san aiki ba da ya bar Najeriya lokacin Shugaba Buhari ba ya kasar. Bayan nan kuma ta soki Matar Shugaban Kasa watau Hajiya Aisha Muhammadu Buhari a gaban Duniya.
KU KARANTA: Ana cigaba da kashe-kashen hauka a Jihar Zamfara har gobe
A dalilin haka ne dai aka kori wannan mata daga bakin aikin ta domin kuwa sukar na ta ya sabawa ka’idar aikin Gwamnati. Gwamnan na Gombe dai ya roki Gwamnatin Tarayya tayi hakuri ta sake duban lamarin a maido wannan mata aikin ta.
Sai dai wasu sun ce a Jihar Gombe ma an taba korar wani daga aiki saboda ya soki Mahaifiyar Gwamna Ibrahim Dankwambo. Gwamnan dai yace ya sa an yi bincike kan lamarin kuma aka maida wannan Bawan Allah bakin aikin sa a lokacin.
Kwanaki kun ji cewa Gwamnan na Gombe da ke neman shugaban Kasa yayi wa Matasan Najeriya alkawari cewa idan har Jam’iyyar PDP ta kuma samun mulkin Kasar nan a zaben 2019 to lallai za ta tafi da Matasa masu jini a jika a Gwamnati.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng