An janye jami’an tsaron Saraki da Dogara

An janye jami’an tsaron Saraki da Dogara

A jiya ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, na da tambayoyin da zai amsa dangane da ambaton sunan sad a ‘yan fashin da suka yi sata a bankunan garin Offa dake jihar Kwara suka yi.

Rahotanni sun bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sanda kama Saraki bayan gabatar masa da hujjoji a kan sa yayin wata ganada Sifeton ‘yan sanda, Ibrahim Idris, ranar juma’a.

A cigaba da wannan dambaruwa ne, tsagin ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka koma jam’iyyar APC (nPDP) sun bayyana janyewa daga tattaunawa da shugabancin jam’iyyar APC, su na masu bayyana cewar har yanzu akwai mugun nufi a kan ‘yan nPDP dake cikin APC.

An janye jami’an tsaron Saraki da Dogara
Saraki da Dogara

A wani jawabi da jagoran ‘yan nPDP, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, ya fitar ya ce akwai alamar tambaya a cikin batun alakanta Saraki da laifin fashi tare da bayyana shakku a kan manufar gwamnati na janye fiye da rabin jami’an tsaro dake bawa Saraki da Dogara tsaro.

DUBA WANNA: An rerawa mawaki Rarara wakar cinye kudin kungiyar mawaka miliyan N100m

Baraje ya zargi fadar shugaban kasa da amfani da jami’an tsaro domin muzgunawa mambobin nPDP duk da irin gudunmawar da suka bawa jam’iyyar APC hart a kai ga nasara.

A ranar lahadi ne rahotanni suka rawaito cewar hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta janye fiye da rabin jami’an ta dake wa Saraki da Dogara aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel