Lallai auran mata da yawa akwai dadi – Wani Bahaushe ya yabi matansa guda 3 cikin shauki (hotuna)
Kamar yadda addinin musulunci ta tanadar mutun kan iya auran mata biyu ko fiye da haka idan har zai iya yin adalci a tsakaninsu. Saboda haka maza musulmai da dama ke auran mata fiye da daya sannan kuma suna zaman lafiya.
Duk da hakan yak an zamo mawuyacin abui ganin matan sun zauna lafiya da kishiyoyinsu, amma dai wasu lokutan auren mata da yawa kan yi karko.
Wani dan Najeriya mai suna Kabiru Ishaq Sa’id ya nuna yadda auran mata da yawa yayi masa rana . mutumin dake auren mata uku ya yabi matan nasa kan irin gudunmawar da suke basa.
Sa’id ya wallafa hotonsa da na kyawawan matansa guda uku a shafin Facebook, inda yake godiya gare su bisa yadda suka sauya masa rayuwa. Magidancin ya bayyana cewa sun koya masa yadda ake zama jarumi ta wanni fanni a rayuwarsa.
KU KARANTA KUMA: Duk miji da matan da basu san lamban sirri na katin ATM din junansu ba toh ba ma’aurata bane – Mataimakin kwamishinan yan sanda
Ya kuma nuna tsantsar soyayya ga matan nasa inda ya bukaci su yafe masa a duk inda ya saba masu.
Ga yadda ya wallafa a shafin nasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng