Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani

Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani

A wani sabon salo na adawar siyasa dake ruruwa a jihar Kaduna, musamman a tsakanin tsagin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da na Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, an samu furucin kalaman tunzura da batanci.

Legit.ng ta ruwaito a wani dan majalisar dokokin jihar Kaduna dake wakiltar al’ummar karamar hukumar Igabi ta yamma, kuma guda cikin na hannun daman gwamnan jihar Kaduna, Honorabul Yusuf Zailani ya sanya kyautar miliyoyin kudi ga duk wanda ya kawo masa gashin Shehu Sani.

KU KARANTA: Ruwa yayi tsami: Hukumar tsaron sirri ta janye jami’anta dake tsaron Saraki da Dogara

Zailani, mai tsawatarwa a majalisar jihar ya bayyana wannan magana ne a yayin wani taron yan siyasa magoya bayan gwamna El-Rufai da aka shirya a gundumar Rigasa na jihar Kaduna. inda yace: “Duk wanda ya asko min gashin Sanata Shehu Sani kuma ya kawo min gashin zan bashi kyautar kudi naira miliyan 5!”

Wani dan majalisa ya sanya tukuicin N5,000,000 ga duk wanda ya yanko masa gashin Shehu Sani
Shehu Sani da Yusuf Zailani

Shi dai Sanata Shehu Sani ya yi suna wajen tara gashi akansa, wanda aka fi sani da Ciko ko Afro da harshen Turanci, tun fiye da shekaru 15 da suka gabata, don haka gashin ta zama wata alama ta gane Sanatan a duk inda ya shiga.

Sai dai har zuwa yanzu Sanatan bai ce uffan ba game da kwangilar farautar gashin nasa da dan majalisa Yusuf Zailani ya bayar, amma masana siyasa sun yi Allah wadai da wannan magana, inda suka ce hakan ka iya jefa rayuwar Sanatan cikin hadari.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng