Kishin-kishin: Shugaba Buhari ya amincewa sifeton 'yan sanda kama Saraki
A yau, Lahadi, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar a shirye yake ya karrama gayyatar da hukumar da ‘yan sanda tayi masa dsa zarar takardar gayyatar ta same shi.
Kazalika, Saraki ya musanta cewar akwai wata alaka dake tsakanin sa da mutanen da ake zargi da aikata laifin fashin bankunan garin Offa na ranar 5 ga watan Afrilu.
Ayau, Lahadi, ne hukumar ‘yan sanda ta bayyana cewar wasu daga cikin wadanda ta kama dangane da batun fashin bankunan garin Offa sun ambaci sunan Saraki da na gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, a matsayin mutanen dake daukar nauyin aiyukan sun a ta’addanci.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana cewar shugaba Buhari ya lamuncewa shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya , Ibrahim K. Idris, kama Saraki bayan gabatar masa da shaidar samun hannun Saraki a cikin aiyukan ta’addanci, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.
DUBA WANNAN: Sunayen ‘yan ta’addan da ‘yan sanda ke zargin Bukola Saraki da daukan nauyin aiyukan su
Kakakin shugaban kasa da na hukumar ‘yan sanda sun ki cewa komai a kan wannan batu da kuma ganawar shugaba Buhari da shugaban na ‘yan sanda ta ranar juma’a.
Da yake jawabi cikin snarwar da mai Magana da yawun sa, Yusuph Olaniyonu, ya fitar, Saraki y ace alakanta shi da fashi wani makirci ne kawai na bata masa suna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng