'Yan sanda sun cafke wasu Mutane 3 masu garkuwa da Mutane sanye da Kakin Sojin Kasa a Jihar Osun

'Yan sanda sun cafke wasu Mutane 3 masu garkuwa da Mutane sanye da Kakin Sojin Kasa a Jihar Osun

Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sandan jihar Osun, ta samu nasarar cafke wasu mutane uku masu garkuwa da mutane; Henry Omenihu, Paul Chituru da Henry Bright da suka saba gudanar da ta'addancin su sanye cikin tufafi na Kakin Sojin Kasa.

Kamar yadda shafin Jaridar The Trust ta ruwaito, Kwamshinan 'yan sanda na jihar, Mista Fimihan Adeoye shine ya bayyana hakan a babban ofishin su dake birnin Osogbo yayin ganawa da manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata.

Kwamishinan na 'yan sanda ya bayyana cewa, wadannan 'yan ta'adda sun yi garkuwa ne da wani Mista Kayode Agbeyangi da kuma Misis Oyeyemi Obafemi a kan babbar hanyar Ilesa zuwa Ibadan tun a ranar 14 ga watan Afrilun 2018.

Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya afku ne yayin da wadanda abin ya shafa suka tsahirta da tafiyar su domin sauya tayar motar su kirar Toyota Camry, inda ba su yi aune ba miyagun suka hallara cikin bazata yayin da suka fito daga Daji sanye da Kakin Sojin kasa kuma suka yi awon gaba da su.

'Yan sanda sun cafke wasu Mutane 3 masu garkuwa da Mutane sanye da Kakin Sojin Kasa a Jihar Osun
'Yan sanda sun cafke wasu Mutane 3 masu garkuwa da Mutane sanye da Kakin Sojin Kasa a Jihar Osun

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan miyagu sun tsare mutanen biyu da suka yi garkuwa da su har na tsawon kwanaki hudu yayin da suka karbe fansa ta Naira Miliyan biyu a hannun 'yan uwan su kafin su 'yantar da su.

KARANTA KUMA: Lai Muhammad ya bayyana amincin sa dangane da shirin Najeriya na daukar nauyin taron UN

Babban jami'in ya bayyana cewa, sakamakon binciken diddigi da hukumar 'yan sandan ta gudanar ya sanya ta samu nasarar cafke 'yan ta'addan uku bayan sun karbe fansar Naira Miliyan a garin Emuoha dake jihar Ribas.

Ya kara da cewa, an samu nasarar cafke su tare da bindigar AK47 mai dauke da alburusai da kuma Kakin Sojin Kasa har guda hudu da suke basaja da su wajen wannan aika-aika.

A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan mutane uku da ake zargi inda daga bisani za su gurfana gaban Alkali kamar yadda kwamishinan 'yan sandan ya bayyana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng