Abin mamaki: An haifi wani jariri dauke da Kur'ani da carbi a jihar Bauchi, kalli hotuna

Abin mamaki: An haifi wani jariri dauke da Kur'ani da carbi a jihar Bauchi, kalli hotuna

Mun samu labarin wani abin mamaki da ya faru a garin Burga da ke jihar Bauchi inda wata mace ta yi ikirarin cewa ta haifi jariri dauke da Kur'ani mai tsarki da kuma carbi a hannunsa. Hakan ya sa mahaifiyar da jaririnta sun zama abin kalla a garin.

Shafin Inside arewa ya ruwaito cewa matar ta garzaya gidan fitaccen Shaihun Malamin Islama Sheikh Dahiru Usman Bauchi don sanar dashi wannan abin mamakin da ya faru da jaririnta da aka rada wa suna Muhammadu Auwal.

Bayan ta isa gidan Shaihin, matar ta yi rantsuwa da Allah cewa wannan lamari gaskiya ne kuma saboda kawar wa wasu mtane shakku a zuciyarsu duk da cewa abu ne da ya bawa al'umma mamaki.

Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi
Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi

KU KARANTA: Baya ga lalata huhu, likitoci sun gano wasu manyan illoli da tabar cigari ke yiwa dan-adam

A yayin hudubar Juma'a da ya yi a jiya, Shaihin ya ce "wannan ba komai bane a wurin Ubangiji, sai dai raddi ga kafirai masu inkari ga manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) don ya kara tabbatar musu da cewa Allah gaskiya ne.

Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi
Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi

"Bugu da kari, wannan ta kara bayyana wa duniya mu'ujizar manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) saboda haka ne aka haifo wannan jinjirin dauke da Kur'ani da carbi."

Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi
Abin al'ajabi: An haifi wani jinjiri dauke da Kurani da carbi a jihar Bauchi

Kazalika, Shaihin ya kara da cewa carbin da jaririn da aka haifo jinjirin dashi ba komai ba ne illa raddi ga masu kushe Shehu Tijjani da darikar sa ta Tijjaniyya, Allah ya yi amfani da wannan jaririn ne don ya nuna wa duniya dariku gaskiya ne.

Shaihin ya kuma lura cewa akwai alamomin Tijjaniyya a jikin carbin da aka haifi yaron dauke dashi inda ya ce wannan karaman Shehu Tijjani ne ta kara bayyana ga masu inkari ga darikar ta Tijjaniyya.

Daga karshe, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi addua don samun zaman lafiya ga Najeriya tare da yin addua'ar Allah ya kare addinansa da mabiya addinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel