Auren wata mata ya mutu saboda juyawa mijin ta baya a shimfida
Alkalin wata kotun Customary da ke zamanta a Mapo da ke Ibadan, Cif Ademola Odunade ya katse igiyar auren wasu ma'aurata Nurudeen Akinpelu da Folake saboda mijin na zargin matar da juyawa masa baya a shimfida tare da zargin tana cin amanar aurensu.
Ogundade ya bawa mijin rikon yaransu guda biyu da suka haifa a tsawon shekaru 11 da suke tare inda kuma ya gargadi Folake ta kame kanta daga tayar da wata fitina tsakaninsu.
"Idan Folake na bukatar ganin yaran, tana iya zuwa neman izinin yin haka a kotu a ko yaushe," inji Odunade.
KU KARANTA: Allah ne ya hukunta Mohammed Salah saboda kin yin azumi - Malamin Islama
Akinpelu, wanda malamin harshen labarabci ne ya shaidawa kotu cewa matarsa ta saba kauracewa shimfidansu a duk lokacin da ya neme ta.
Ya ce duk lokacin da ya nemi ya kusance ta, sai ta ture shi ta fada masa cewa ya fita ya je wani wurin ya biya bukatunsa.
Akinpelu ya cigaba da fadawa kotu cewa wannan halin matarsa ya fara ne bayan ta haifi yaransu na biyu kuma hakan ya jefa shi cikin mawuyacin hali kuma yana son a raba auren.
Ya kuma shaidawa kotu yadda ya gano wata takardan maganin kayade iyali a cikin jakarta wanda ta karbo daga asibiti, kuma daga baya ya sake ganin wata takardan maganin wanda hakan ya bata masa rai sosai.
"Akwai lokacin da ta sace yaran mu biyu ta yi tafiyarta, sai da nayi shekara daya da rabi ina nemansu.
"Har ta kai ga na kai kara ofishin Yan sanda kafin daga bisani aka dawo min da yara na," inji Nurudeen.
A bangarenta, Folake ta amince da bukatarsa na raba auren kuma bata musanta zargin da ya yi mata ba sai dai ta fadawa kotu cewa tana ziyartar wuraren magani ne a kan duwatsu.
"Nurudeen baya kula da ni da yara na kuma yana yawan duka na duk lokacin da muka samu rashin jituwa," inji Folake.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng