Tsofaffin Gwamnonin da ake zargi da laifin satar dukiyar Jama’a a Najeriya

Tsofaffin Gwamnonin da ake zargi da laifin satar dukiyar Jama’a a Najeriya

Yanzu haka akwai wasu tsofaffin Gwamnonin Kasar nan da ke hannun Hukumomin yaki da satar dukiyan kasa. Mun tsakura wasu daga cikin tsofaffin Gwamnonin Arewacin Kasar da ke shari’a a Kotu.

1. Abdullahi Adamu

Ana zargin tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa anata Abdullahi Adamu wanda yayi mulki daga 1999 zuwa 2007 da laifin lakume wasu Biliyan 15.

2. Ahmad Sani Yerima

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara wanda shi ma yanzu Sanata ne da laifin karkatar da wasu Naira Biliyan 1 lokacin da yake kujerar Gwamna.

3. Joshua Dariye

Hukumar EFCC na zargin tsohon Gwamnan Filato da laifin wawure Naira Biliyan 1.162 na dukiyar Jihar sa lokacin yana Gwamna.

KU KARANTA: EFCC ta garkame tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Yero

4. Ibrahim Shekarau

Bayan tsohon Gwamnan na Kano ya sauka daga mulki ne aka fara zargin sa da raba kudi har Naira Miliyan 950 lokacin zaben 2015.

5. Jonah Jang

Ana zargin wani tsohon Gwamnan na Filato da laifin yin awon-gaba da sama da Naira Biliyan 6 lokacin da yake shirin barin kujerar sa.

6. Saminu Taraki

EFCC na zargin Saminu Turaki na Jihar Jigawa da satar kudin da su ka haura Naira Biliyan 36 lokacin da yayi Gwamna daga 1999 zuwa 2007.

7. Sule Lamido

Ana zargin shi ma Magajin Saminu Turaki da laifin damfarar mutanen Jihar sa kudin da su ka haura Naira Biliyan 1.35.

8. Ibrahim Shema

Ana zargin tsohon Gwamnan Jihar Katsina da laifin yin awon-gaba da sama da Naira Biliyan 5.7 na kudin SURE-P lokacin yana Gwamna.

9. Bukola Saraki

Haka kuma ana zargin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da kin bayyanawa Duniya kadarorin da ya mallaka lokacin yana Gwamna.

10. Attahiru Bafarawa

Ana shari’a da tsohon Gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa inda ake zargin sa da laifin satar Naira Biliyan 15.

11. Murtala Nyako

Tsohon Gwamnan Adamawa yana ganin ta kan sa a Kotu inda ake zargin sa da ‘Dan sa da laifin sace Naira Biliyan 29 na Jihar.

12. Danjuma Goje

Hukumar EFCC na zargin tsohon Gwamnan Gombe da laifin satar kudi har Naira Biliyan 25 a lokacin da yake kujerar Gwamna.

13. Gabriel Suswam

Shi ma dai tsohon Gwamnan Benuwe akwai zargin da ke kan sa na satar kudin Jama’a har sama da Biliyan 3 lokacin da yayi Gwamna.

Kamar yadda Daily Trust ta kawo jerin, sauran tsofaffin Gwamnonin da ake zargi da laifin sata sun hada da:

14. Ahmad Fintiri

15. Micheal Botmang

Kwanan nan ma dai aka fara binciken tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Muktar Ramalan Yero kan zargin cin wasu kudin Talakawa har Naira Miliyan 750 da yayi. Yanzu haka dai an garkame Yero tun jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel