'Tarin ayyuka da bashi da na taras a Jigawa sun kusa kora ta daga gwamna a 2015'
- Gwamnan Jihawa ya waiwaya yadda ayyukan 2015-2018 suka kaya
- Gwamnan yace ya zuwa yanzu kam su a Jigawa sai MashaAllah
- Badaru Talamiz yace kusan guduwa yayi da ya ga bashin da PDP ta bar mas
Badaru Talamiz, dattijon gwamnan Jigawa, wanda ya karbi mulki daga hannu Sule Lamido, ya bayyana yadda ya taras da uban bashi da gwamnatin PDP ta bar masa a yayin mika masa takardun mulki a 2015, inda yace abin ya girgiza shi.
'Kusan barin mulkin ma nayi gaba daya, domin na taras da N16m ne kacal amma bashi da manyan ayyuka da aka faro sun kai akalla na N36b'.
Gwamnan, ya kara da cewa, a yanzu, yaci karfin duk ayyukan da ya taras, kuma ya dauko nasa yana kian yinsu, a hira da 'yan jarida kan bikin ranar dimokuradiyya.
DUBA WANNAN: Ko nPDP sun ki ko sun so shugaba Buhari zai zarce
Gwamna Talamiz, ya kara da cewa, ya zuwa yanzu, shi kadai ke iya tutiya da cewa ba'a bin jiharsa uban bashi, sai dai abin da ba'aa rasa ba, kuma yana iya iya biyan ma'aikatansa albashi a 25 ga kowanne wata na shekara.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng