Majalisar Dinkin Duniya ta ba Farfesa Ibrahim Gambari wani babban aiki

Majalisar Dinkin Duniya ta ba Farfesa Ibrahim Gambari wani babban aiki

- Majalisar Dinkin Duniya na UN ta nemi Farfesan Najeriya yayi mata wani aiki

- Ibrahim Gambari ‘Dan asalin Jihar Kwara dai ya kara fito da Najeriya a Duniya

- Tsohon mai shekaru 73 yana cikin kwamitin da za su duba yarjejeniyar Durban

Labari ya zo mana yau cewa Majalisar Dinkin Duniya ta ba wani babban Farfesa da ake ji da shi a Najeriya wani aiki na musamman. Wannan dai ba kowa bane sai Farfesa Ibrahim Gambari.

Majalisar Dinkin Duniya ta ba Farfesa Ibrahim Gambari wani babban aiki
Farfesa Ibrahim Gambari lokacin da ya kai ziyara Kasar Sudan a baya

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Farfesa Gambari cikin wani kwamiti na kwararru da za su duba yadda za a dabbaka yarjejeniyar da aka cin ma na Durban a Sudan. Wani babban Jami’i na UN Ra’ad Al-Husseini ya bayyana wannan Ranar Juma’a.

KU KARANTA: Yadda aka cirewa Budurwa samarin Aljanun da ke kan ta

Jami’ar Jihar Kwara da ke Garin Malete inda Farfesan ya ke aiki ta sanar da cewa an nada Ibrahim Gambari cikin wannan kwamiti na Majalisar dinkin Duniya. Sauran wadanda ke cikin kwamitin sun hada da wasu Turawa da wasu Yankin.

Shugaban Jami’ar ta Kwara Farfesa Abdurrasheed Na’Allah ya nuna jin dadin su game da wannan gagarumin aiki da Farfesa Ibrahim Gambari ya samu domin kawo cigaba da zaman lafiya a Yankin na Sudan da ma dai daukacin Duniya.

Ibrahim Gambari Tsohon Ministan Kasar waje ne na Najeriya a lokacin mulkin Soja na Janar Buhari tsakanin 1984 zuwa 1985. Gambari ya dade yana aiki da Majalisar Dinkin Duniya kuma tsohon Malami Makaranta ne tun shekarar 1969.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng