Za a cigaba da shari'ar tsohon Gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame

Za a cigaba da shari'ar tsohon Gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame

- Yau ake sa rai a gama shari’a tsakanin EFCC da tsohon Gwamnan Taraba

- EFCC na zargin Rev. Jolly Nyame da lakume wasu kudi sama da Biliyan 1.6

- Lauyan EFCC na neman babban Kotun Tarayyar ta daure tsohon Gwamnan

Labari ya zo mana cewa wani babban Kotun Tarayya da ke Abuja zai zauna yau domin cigaba da shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Taraba watau Rabaren Jolly Nyame wanda yayi mulki daga 1999 zuwa 2007.

Za a cigaba da shari'ar tsohon Gwamnan Jihar Taraba Jolly Nyame
EFCC ta tasa tsohon Gwamnan Taraba Jolly Nyame a gaba

Ana sa rai yau za a kammala shari’ar Jolly Nyame wanda ake zargi yayi gaba da sama da Naira Biliyan 1.6. Tun 2010 ne dai Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ta fara maka tsohon Gwamnan a Kotu.

KU KARANTA: Wasu 'Yan bindiga sun yi barna a cikin Jihar Kaduna

Hukumar EFCC na sa ran Kotu ta daure tsohon Gwamnan bayan Lauyan ta Rotimi Jacobs SAN ya gabatarwa Kotu shaidu 14. Sai dai Olalekan Ojo watau Lauyan da ke kare tsohon Gwamnan yace babu gaskiya a shaidun da EFCC ta bada.

Shi dai Alkali mai shari’a Adebukola Banjoko a wancan lokacin ya dage karar ne zuwa yau. Tun farkon shekarar nan dai ake jiran a karasa wannan shari’a. Tsohon Gwamnan dai yace bai saci ko kobo na Jihar Taraba ba lokacin da yake Gwamna.

Dazu kun ji cewa Matar Tsohon Shugaban Alkalai gaba daya na Najeriya Mahmood Muhammad sun rasu a wani mummunan hadarin mota tsakanin Birnin Tarayya Abuja zuwa Garin Kaduna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel